Ƙungiyar masu harkar fina-finai ta Najeriya MOPPAN, ta ja kunnen ƴan Kannyowood da su daina yi wa juna bankaɗa da tone-tonen asiri a ko ina musamman a shafukan sada zumunta, biyo bayan ce-ce-ku-cen da ya ɓarke a ƴan kwanakin nan a masana’antar.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar wacce BBC ta samu mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawunta Al-Amin Ciroma, ta ce ta yanke shawarar jan kunnen ƴaƴan ƙungiyar ne a yayin da ake ci gaba da tafka tsattsamar mahawara dangane da rigingimun da suka biyo bayan tattaunawar da BBC Hausa da Hajiya Ladin Cima.

“Mun lura lamarin na ɗaukar wani salo na daban. Har ila yau, zancen na ci gaba da jan hankalin al’umma, musamman mabiya al’amuran fina-finan Hausa, inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa dangane da zancen.

“Hakan ta sa wasu masu ruwa da tsaki suka fara kiraye-kiraye ga shugabannin MOPPAN, da su shiga su magance muhawarar,” in ji sanarwar.

MOPPAN ta ƙara da cewa mutane da ƙungiyoyi da dama sun aika mata buɗaɗɗun wasiƙu kan cewa ta tsawatar kan lamarin.

Shugaban MOPPAN na ƙasa Dr. Ahmad Muhammad Sarari ya ce sanin muhimmancin kiraye-kirayen ne ya sa ƙungiyar ke tabbatar wa al’umma cewar ta ɗauki ƙwararan matakai, da hadin gwiwar sauran kungiyoyi, kamar kungiyar masu shirin fim ta Arewa, wato AFMAN dangane da lamarin.

Baya ga ganin sanarwar, BBC ta sake tuntuɓar mai magana da yawun MOPPAN Al-Amin Ciroma, wanda ya ce lamarin na ƴan Kannyowwod na neman wuce gona da iri.

“Abu ya faru kan hirar da aka yi da Ladin Cima amma sai jan magana suke ta yi har hakan ta sa an shiga wata gaɓar ta zarge-zarge da jifa juna da kalamai marasa daɗi.

“Mafi ban takaici shi ne yadda suka bazama shafukan sada zumunta irinsu Tiktok da Instagram da Facebook, wurare marasa sirri suna takalar juna,” in ji shi.

Ciroma ya ci gaba da cewa dole ne MOPPAN ta taka musu burki saboda abin nasu ya koma kai wa juna hari da jifan juna da gore-gore da zarge-zarge da kalaman ɓatanci.

Waɗanne matakai MOPPAN ta ɗauka?

Ƙungiyar MOPPAN dai ta ce ta ɗauki wasu matakai kan wannan lamari, daga cikinsu akwai jawo hankalin dukkanin ɓangarori da su dakata da musayar yawu.

Haka kuma, MOPPAN za ta cimma matsaya ta musamman kan lamarin, bayan shirye-shirye da dama da ta gudanar.

A ƙarshe, shugabannin kungiyoyin suna kara kira ga dukkanin ƴaƴan Kannywood da su kasance masu kishin masana’antar, su kuma daina bin son zuciya da zai iya kawo manyan matsaloli ga sana’ar fim baki ɗaya.

MOPPAN tana kira da a yaɗa wannan magana a kowace kafar yada labarai da sadarwa.

Haka kuma MOPPAN za ta cimma matsaya bayan kammala tattaunawa da sauran ƙungiyoyi da masu ruwa da tsaki a harkar da kuma dattijai.https://www.bbc.com/ws/av-embeds/cps/hausa/labarai-60226161/p0bn640x/haBayanan bidiyo,

…Daga Bakin Mai Ita tare da Ladin Cima

Me ya faru tun farko?

A makon da ya gabata ne ce-ce-ku-ce ya ɓarke kan batun yawan kudin da ake biyan ‘yan fim a masana’antar shirya fina-finan ta arewacin Najeriya, bayan da Ladin Cima ta ce ba a taɓa biyanta sama da 20,000 ba a fim a hirarta da BBC Hausa a shirin Daga Bakin Mai Ita na ranar Alhamis.

Ainihin hirar an yi ta ne ranar Lahadi 14 ga watan Nuwamban 2021, a lokacin da BBC ta aika ma’aikatanta biyu Kano don tattaro shirin Daga Bakin Mai Ita da wasu ‘yan Kannywood 11.

Amma da yake ana saka shirin daya bayan daya ne a kowace Alhamis, shi ya sa na Ladin Cima bai fito ba sai bayan wata biyu da yin hirar.

Wannan magana ce ta ja hankalin masu bin shafukan BBC Hausa na intanet inda suka dinga zargin furodusoshi da daraktoci da rashin tausayin tsofaffin ‘yan fim din.

Lamarin da ya sosa ran wasu furodusoshin irin su Ali Nuhu da Falalu Dorayi, har suka shaida wa BBC cewa ko su sun taba ba ta kudade masu yawa na fita a fim dinsu da ta yi.

Daga baya lamarin ya ɗauki sabon salo inda ƴan fim da dama suka fito wasu suna zargin Tambaya da rashin godiyar Allah, wasu kuma suna cewa abin da ta faɗa gaskiya ne.

Bayan haka ne kuma sai aka fara ƴar tne-tone da zarge-zarge a tsakanin ƴan masana’antar.

bbc hausa

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan