Ɗan Majalisar dokokin jihar Zamfara, ɗaya tilo daga jam’iyyar PDP mai adawa, ya koka a kan barazanar da ya ce ana yi masa kwanaki ƙalilan bayan majalisar ta amince a ci gaba da yunƙurin tsige mataimakin gwamnan jihar.
Hon. Salihu Usman Zurmi, ya shaida wa BBC cewa fargabar barazanar ce ta tilasta masa tserewa zuwa gudun hijira a wajen jihar.
Dan Majalisar ya ce, “Ina fuskantar barazana ce ta kamu a kan rashin amincewa da ci gaba da yunkurin tsige mataimakin gwamna abin da ya janyo mini wata matsala ga gwamnatin jihar wadda ke ganin zan zameta karfen kafa”.
A don haka gwamnatin ke ganin kama ni ko tsare ni zai bata damar cimma burinta na ci gaba da yunkurin tsige mataimakin gwamna, in ji dan majalisar.
Hon. Salihu Usman Zurmi, ya ce,” A gaskiya duk da ya ke ba a kai ga kamani ba, to ni ina zargin cewa gwamnati ce ta bayar da umarnin a kama ni”.
Hon. Salihu Usman Zurmi, ya ce, “Wannan daliline na kishin jam’iyyata ya sa na fara magana da ‘yan majalisa ‘yan uwana na nuna musu illar yarda ayi amfani kai don musgunawa wani, domin duk abin da ka yi kai ma a gaba sai an yi maka”.
Ya ce, “To shawarwarin da nake bayarwa ne ya sa har gwamnati ta ji su sannan ta fara bin diddigi don jin abin da nake cewa a Majalisar da ake gani kamar ina nema na ja ra’ayinsu”.
To tuni dai mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Zailani Bappa, ya shaida wa BBC cewa babu ƙanshin gaskiya kan wannan zargi saboda Gwamna Bello Matawalle, ba ya katsalandan cikin harkokin Majalisar jihar, don haka babu ruwansa cikin duk wani batu da ya shafi aikinta, balle har ya yi wa wani ɗan majalisar barazana.

Karin bayani
A ƙarshen watan Yuni ne gwamnan jihar Zamfara Mohammed Bello Matawalle ya sauya sheƙa daga babbar jam’iyyar hamayya ta PDP zuwa ta APC mai mulkin ƙasar.
Sai dai mataimakin nasa, Barrister Mahdi Aliyu Gusau, bai sauya sheƙa tare da ubangidansa ba ya ci gaba da zama a jam’iyyar PDP.
A lokacin, mataimakin gwamnan ya nuna cewa babu wata hamayya da za ta taso a tsakaninsu duk da cewa a yanzu ba sa jam’iyya guda.
Asali ma, mataimakin gwamnan ya bayyana cewa dama al’ummar jihar zamfara ce ta zaɓe su don su yi masu aiki kuma yana fata hakan za su ci gaba da yi.
Haka kuma, mataimakin gwamnan ya shaida wa BBC a wata hira ta musamman cewa ba shi da niyyar sauya sheƙa zuwa APC, kuma ba ya fargabar tsigewa daga majalisa.
bbc hausa