Hukumar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA) ta ce tana neman ɗan sanda DCP Abba Kyari ruwa a jallo kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi.
Wata sanarwa da NDLEA ta fitar a yau Litinin ta ce bincikensu ya nuna cewa Abba Kyari na da alaƙa da wata ƙungiya da ke safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasashen Brazil da Ethiopia zuwa Najeriya.
Ta ƙara da cewa jami’an NDLEA sun gayyaci ɗan sandan don ya amsa tambayoyi game da zarge-zarge amma ya ƙi zuwa, “abin da ya sa muka yi wannan taron manema labaran kenan”.
“Ƙin amsa kiran hukumarmu da ya yi da ƙin ba mu hadin kai wajen bincike shi ne dalilin da ya sa muka yi taron manema labaran nan a yau.”
Idan ba a manta ba, a watan Yulin 2021 ne rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta dakatar da DCP Abba Kyari mai muƙamin kwamishinan ‘yan sanda bisa zargin karɓar cin hanci daga Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppid – mutumin da ke tsare a Amurka bisa zargin damfarar miliyoyin dala.
NDLEA ta kamen da aka yi da yawan mutanen da aka tsare a cikin wata 12 da suka gabata alama ce da ke nuna cewa a baya an raina girman matsalar tu’ammali da miyagun ƙwayoyi da ƙasar ke ciki, kafin Shugaba Buhari ya ƙarfafa hukumar NDLEA.
Amma ta ce a cikin wata 12 mafi yawan ƴan Najeriya sun yarda cewa ƙasar na cikin wata masifa ta tu’ammali da miyagun ƙwayoyi kuma suna yaba wa ayyukan NDLEA don daƙile hakan.
Sanarwar ta ce sai dai abin takaicin shi ne yadda wasu jami’an tsaron da ya kamata su haɗa hannu da NDLEA wajen daƙile wannan annoba su ne a gaba-gaba wajen karya dokar, ta wajen haɗa kai da su ana safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasar.
Bayanan sirrin da muka samu sun sa hukumarmu ta yarda ɗari bisa ɗari cewa DCP Kyari ɗaya ne daga cikin masu safarar miyagun ƙwayoyi tsakanin Brazil da Ethiopia da Nigeria, kuma yana buƙatar amsa tambayoyin da suka bijiro a kan wani batun safarar ƙwayoyi da yake jagoranta.
‘Yadda muka bankaɗo asirin Abba Kyari’
Sanarwar ta ce lamarin ya fara ne a ranar Juma’a 21 ga watan Janairun 2022 a lokacin da DCP Kyari ya kira wani jami’in NDLEA cewa zai je ofishin hukumar na Abuja da misalin ƙarfe 2.12 na rana amma bai ɗauki wayar ba.
Daga baya jami’in ya kira Kyarin, inda ya ce masa dama yana son zuwa ofishin NDLEA din ne don tattauna wani batu na aiki bayan Sallar Juma’a.
Daga bisani Kyari ya je ofishin ya kuma ce ya je ya gaya musu cewa tawagarsa ce ta kama wasu masu safarar ƙwayoyi da suka shiga Najeriya daga Habasha da koken har kilo 25.
Sai ya nemi jami’in NDLEA ɗin da ya ba shi hadin kai don shi da tawagarsa su ɗauki kilo 15 sai a miƙa wa hukuma kilo 10 don shigar da waɗanda aka kama da hodar ƙara a Enugu.
“A yanzu dai za mu musanya kilo 15 na hodar ibilis ɗin a cikin buhunhunan bogi,” in ji Abba Kyari kamar yadda sanarwar NDLEA ta ambato.
Sannan ta ce sai Kyarin ya nemi jami’in NDLEA din da ya shawo kan jami’ansu da su ba da hadin kai.
A ranar Litinin 24 ga watan Janairu da misalin karfe 11.05 na safe ne NDLEA ta bai wa jami’inta umarnin biye wa Abba Kyari don zurma shi kan buƙatarsa.
Daga nan sai shi da Abba Kyari suka fara magana ta hanyar kiran wayar Whatsapp. Jami’in sai ya biye masa don ganin gudun ruwansa.
“An kasafta ta an yi cinikinta“
A wannan gabar ce Kyari ya ce tuni aka cire kilo 15 na koken din aka raba wa mutanen da suka kawo labarin da kuma shi da tawagarsa.
A cewarsa an bai wa waɗanda suka kawo labarin kilo 7 shi da tawagarsa kuma suka ɗauki kilo 8 wanda tuni suka sayar.
Sai kuma ya buƙaci biyan jami’in NDLEA na ofishin Abujan da kudin da za a sayar da sauran kilo 10 a madadinsu, lamarin da ya sa yawan koken ɗin da za a shigar da ƙarar ya ragu ya koma kilo biyar.
Hukumar NDLEA ta ci gaba da cewa kowane kilo ɗaya ne na koken yana kamawa a kan naira miliyan bakwai.
A alkawarin da ya yi, ya ce zai bai wa tawagar NDLEA dala 61,000 kwatankwacin naira miliyan 34.7.
Sai kuma ya matsa wa jami’in NDLEA na ABuja lamba cewa lallai ofishinsa ya jagoranci kula da koken din da mutanen da aka kama su da shi.
“A lokacin yana magana ne daga Lagos, inda ake zargin ya je ne don gabatar da wasu al’amuran kasuwanci na ƙashin kansa.
“A washegarin ranar 25 ga Janairu sai Kyari ya tura ƙaninsa don kai kuɗin yayin da jami’an tawagarsa kuma suka kai waɗanda aka kama da koken din, amma sai jami’inmu ya ƙi yarda da hakan, ya dage cewa ya fi so ya yi mu’amala kai tsaye da shi Kyarin don haka suka tsara haɗuwa a Lagos.”
Yadda aka naɗi abin da Kyari ya yi
A tattaunawarsu ya bayyana yadda wani daga cikin ayarinsa ya samu bayanai daga wani mai neman cin tudu biyu da ya yaudari masu safarar ta wajen ba shi bayanai, inda ya nuna masa wasu cikakkun shaidu na alaƙa tsakanin jami’an tsaro da kuma gagga-gaggan masu safarar miyagun ƙwayoyi.
Ya bayyana yadda ayarin ma’aikatansa da aka tsegunta musu bayanan suka tashi daga Abuja suka je Eungu suka kama masu safarar, suka ɗauke wasu daga cikin kayayyayin suka zuba na bogi a madadinsu.
Sai ya aika hoton ainihin ledar da koken ɗin ke ciki. A yadda aka tsara shirin, idan har aka gwada kilo biyar na koken ɗin ainihin aka ga daidai ne, to babu buƙatar gwada sauran ledojin bogin da aka zuba wani abin daban.
Ya kuma tafi da kuɗaɗen da aka sayar da kilo biyar na koken ɗin wato rabon jami’an NDLEA dala 61,400.
Amma sai jami’inmu ya nuna buƙatar ya fi son ya karɓi kuɗin a cikin motarsa, wacce tuni aka tsara mata abubuwan naɗar murya da bidiyo.
Hukumar NDLEA ta nuna manema labarai bidiyon da wajen taron da ta kira ranar Litinin 14 ga watan Fabrairun 2021.
Muna da isassun hujjoji
NDLEA a sanarwata ta ci gaba da cewa tana da tarin hujjoji na bayanan sirri da suka haɗa da hotuna da bidiyo da hirar chatin tsakanin Kyari da jami’insu.
“Ba za mu iya bayanin dukkan abubuwa ba a nan. Sai dai abin takaici ne yadda aka samu aka kama jami’in tsaro dumu-dumu da karya doka tare da ayarinsa da har yake ikirari yana cewa: “yaran suna da ƙwazo sosai-sosai kuma suna da amana.”
“Sannan kuma abin takaici ne yadda aka jiyo shi yana kiran wannan ayari nasa da cewa: “Ina kula da su sosai, kuma wannan tawagar ce kawai take wannan aikin.
“Har da ma buɗar baki yana fadar yadda suka yi wani aikin irin wannan mako uku kafin wannan.
“To ba mu tara mutane don kwance masa zani a kasuwa ba. Amma ina so mu gane abin da ya kawo mu wannan gaɓa har muke taron manema labarai,” sanarwar ta ƙara da cewa.
NDLEA ta ce a yanzu haka hodar ibilis din da mutanen da aka kama da ita suna hannun hukumar tun ranar 8 ga watan Fabrairu, amma har yanzu ba a kammala aikin ba don ba ta samu tattaunawa da Abba Kyari ba.
bbc hausa